Yadda Zakayi Amfani Da First Bank Transfer Code  *894# Tura Kudi Ko Recharge Airtime

Assalamu alaikum masu bibiyar wannan website, Kamar yadda muke kawo muku abubuwa masu matukar amfani akoda yaushe musamman wanda suka shafi Technology.

Yauma munzo muku da wani abu mai muhimmanci ga wanda suke amfani da First Bank In Nigeria,

Abin daza kukoya yau shine Yadda Zakayi Transfer Money — Recharge Airtime Da First Bank Transfer Code.

First Bank yana daya daga cikin manyan bankuna dasuke Nigeria, mutane sun yarda da aikinsu da inganci da nagarta dasuke da ita.

First Bank yana da wasu lambobi wato First Bank Transfer Code (*894#) wanda ake amfani dasu wajen tura kudi Transfer Money ko sayen katin waya Recharge Airtime domin samun sauki ga masu amfani da bankin.

Da First Bank Transfer Code cikin sauki zaka iya tura kudi daga bankin first bank zuwa wani first bank ko daga first bank zuwa wani banki daban,

Sannan da wannan code (*894#) zaka iya sayen katin waya zuwa layinka dake Nigeria kamar: MTN, Airtel, Glo, 9Mobile da sauransu.

Atakaice hanyace mafi sauki wajen amfani da First Bank Transfer Code domin rage zirga — zirga wajen zuwa banki domin tura kudi ko zuwa shagon sayar da recharge card domin sayen katin waya.

Yadda Zakayi Register Domin Amfani Da First Bank Transfer Code

Kafin fara amfani da wannan code *894# dole sai kayi Register sannan ka kirkiri wasu lambobi na sirri domin yin abin cikin tsari da kuma tsaro,

A Yanzu sai kabi abin dazamu nuna maka domin yin Register First Bank Transfer Code.

* Kadanna *894*0# akan wayarka da layin da aka bude account dashi.

* Zakaga inda zaka saka lambobi guda 4 na ATM Card wanda aka hada dashi lokacin da aka bude maka account.

* Sannan zaka zabi lambobi guda 4 amatsayin Personal Identification Number (PIN) wannan pin dashi zakana transfer ko sayen Recharge Card.

* Wajen zabar PIN Number kakula domin zabar mai sauki domin kada kamantashi, Sannan kada kabari wani yasan dashi domin zai iya cire maka kudi dashi batare daka saniba.

Idan kabi wannan abin damuka nuna akarshe zakaga alamar kayi Register da First Bank Transfer Code kuma zaka iya amfani dashi akoda yaushe Dare — Rana.

First Bank Transfer Code
First Bank Transfer Code

Yadda Zakayi Transfer Money Da First Bank Transfer Code Daga First Bank Zuwa First Bank Ko Wani Banki Daban

* Kadanna *894*, adadin kudin dazaka tura, account number wanda za’a turawa kudin, kamar dai haka:

*894*Amount*Recipientaccountnumber# sai katura da layin dakayi register dashi.

* Zakaga inda zaka zabi bankin dazaka turawa kudin Misali: UBA, First Bank, GTB da sauransu.

* Zakaga inda zaka tabbabtar da suna da kuma account na wanda zaka turawa kudi, indan kayi Confirm babu wata matsala shikenan.

* Akarshe zakaje inda zaka saka PIN Number domin tabbatar da Transfer sai kasaka lamobobin daka zaba wajen yin Register da First Bank Transfer Code sai katura,

Zaka samu sako daga First Bank cewa Transfer tashiga ko batashiga ba.

Yadda Zakayi Recharge Card Da First Bank Transfer Code

Idan kana son sayen katin kiran waya daga account dinka na First Bank babu wata wahala aciki,

Zaka iya sayen katin daga account dinka dake First Bank zuwa layin daka bude account din dashi kokuma zuwa wani layin waya daban.

* Idan zakayi Recharge Card zuwa layin daka bude account dashi, Kawai zaka danna *894* adadin Recharge Card din daza kasaya,

kamar dai *894*100# sai katura zakaga inda zaka saka PIN Number kana sakawa zakaji kudin yashiga layinka.

* Idan kuma lambar dazaka turawa daban take sai kadanna

*894*100*07067557575# idan katura zakaga inda zaka saka PIN Number kana sakawa kudin zai shiga.

Yadda Zaka Duba First Bank Account Balance

Domin duba adadin kudin dake account dinka na First Bank kawai zaka danna *894*00# zakaga adadin kudin dake cikin asusunka na First Bank.

Da First Bank Transfer Code zaka iya abubuwa dayawa wanda badan wannan Code ba sai kasha wahala wajen zuwa banki da kuma bin layi saboda cukowa,

Don haka idan baka amfani da (*894#) to yanzu ya kamata kafara domin samun sauki.

First Bank Transfer Code Shorts Code

Wadannan jerin lambobi ne da aka gajartasu domin yin amfani ciki sauri,

Maimakon bin dogon jeri wajen yin amfani da First Bank Transfer Code wannan jeri zai taimaka wajen saurin zuwa inda kakeson isa idan kana amfani da (*894#) gasu kamar haka:

* Domin Yin Register: *894*0#

* Domin Airtime Recharge Zuwa Layinka: *894*amount#

* Domin Airtime Recharge Zuwa Wani Layin Waya: *894*amount*number#

* Domin Money Transfer: *894*amount*accountnumber#

* Domin Duba Account Balance: *894*00#

Wannan shine bayanin dazamu iyayi atakaice game da First Bank Transfer Code muna fatan wannan rubutu zai amfaneku.

Sannan idan akwai abin daba kugane ba zaku iya yin Comment akasan wannan rubutu kokuma zaku iya join da shafin HausaTechs.Com dake Facebook Click Here domin karin bayani.

Zaku iya tura mana sako ta watsapp da wannan Number 07066870719. Mungode

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *