Isah Ali Pantami ‘Abinda Yasa Suke Ce Min Dan Ta’adda’

Wata jarida ta buga labarin cewa Ministan sadarwa Isah Ali Pantami yana da alaka da kungiyar ta’adda a Nigeria, sai dai pantami ya karyata wannan batu kuma yafadi dalilin dayasa akayi masa wannan kazafi.

Kamar yadda jaridar ta watsa labarin tace itama tasamu masaniya ne daga wani wajen, cewar pantami yana daga cikin masu tallafawa kungiyoyin ta’adda dake Nigeria.

Sai dai Ministan yace kazafi akayi masa kuma yana da nasaba da jajircewa dayayi don kowa ya mallaki National Identity Number (NIN), wanda hukumarsa tace dole sai kowa yahadashi da layin wayarsa kokuma a rufe layin.

Isah Ali Pantami Yabada Umarnin Hada Layin Waya Da NIN

A karshen shekarar 2020 Minista Isah Ali Pantami yabada umarnin hada layin waya da NIN, kuma aka bada wani wa’adi idan masu amfani da layukan waya dake Nigeria basuyi hakan ba za a rufe layukan wayarsu.

Lamarin yajawo mutane dadama yin rejisatar NIN wanda dama can basu dashi, A cewar Pantami hakan shi yajawo masu adawa da wannan shiri yi masa kazafin ta’addanci kuma hakan bazai hanashi karasa wannan aiki daya dauko ba.

‘Abinda Yasa Suke Ce Min Dan Ta’adda’ Isah Ali Pantami

isah ali pantami

Legit.Ng ta rawaito ministan yace, “Bana kokwanto akan abinda nafada, cemin dan ta’adda yana alaka da yin katin zama dan kasa. yace anfara wannan tsarin a shekarar 2011 amma ba ai nasara ba, saboda akwai wanda suka yaki abin.”

Yacigaba da cewa, akwai wanda sukayi niyyar kawar da wannan batu na yin NIN ga ainihin yan Nigeria da kuma baki mazauna kasar,

Ministan yace anjima ana kokarin kaddamar da wannan tsarin tun shekarar 2015 amma ba ayi nasara ba, yanuna cewa duk lokacin da akayi kokarin kawo tsarin wasu tawaga sai su takawa tafiyar birki.

“Amma abinda basu fahimta ba shine, yin NIN bata yan Nigeria ne kadai ba harda wanda ba yan kasar ba,” Inji pantami. sannan kuma yace hare hare bazai hanashi karasa wannan aiki ba.

Bayan dai zargin Isah Ali Pantami da ta’addanci wasu mutane dadama sunce hakan ba abin mamaki bane, domin dama lokacin dayayi wa’azi a shekarun baya dasuka gabata yakasance Malami mai tsaurin ra’ayi.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *