Hukumar NCC Tahana MTN Da Airtel Glo Sayar Da Sabbin Layukan Waya

Wata sanarwa daga hukumar sadarwa ta Nigeria wato Nigerian Communications Commission (NCC)

Zuwa MTN Da Airtel Glo da sauransu, ta hana duk wani kamfanin sadarwa kamar MTN, Airtel, Glo sayar da sabbin layukan waya har zuwa wani lokaci.

Umarnin wanda aka aikeshi a wasika zuwa ga duk wani kamfanin sadarwa dake Nigeria ya bayyana cewa hukumar ta dakatar da yin Register sabon layin waya har sai sun kammala wani bincike da sukeyi.

A wani labari da Legit ta rubuta ya nuna cewa sanarwar ta fito ne daga Ministan sadarwa wato Dr Isah Ali Pantami,

Hukumar tace yazama dole kamfanonin sadarwar subi wannan umarni.

Hakan yana biyo bayan hare haren ta’adanci da suka yawaita a Nigeria wanda NCC take zargin akwai gudummawar layuka marasa regista da ake sayarwa,

Dakatarwar zata bawa NCC damar binciken layunkan domin tantace wanda suka halatta ayi amfani dasu da kuma wanda suka saba ka’ida.

Aqarshe Hukumar ta gargadi duk kamfanin dabai bi wannan umarni ba zasu iya kwace lasisin gudanar da ayyukansa,

“Yanzu layukan waya marasa regista sun karade gari wanda dasu ake amfani wajen aikata mugayen laifuka”. Inji daraktan hulda da jama’a na NCC, Ikechukwu Adinde.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *