Godaddy Custome Domain, Yadda Zaka Sayi .Com Da Farashin N19000

Assalamu alaikum dafatan mabiya wannan website kuna cikin koshin lafiya Allah yasa haka amin, Kamar yadda muka saba kawo muku hanyoyi daza kubude website ko blog dakuma ingantashi.

Yau zamu nuna muku wata hanya mai muhimmanci wajen Bude Website Ko Blog domin wannan abin daza mu nuna ayau shine mataki nafarko dazaka fara inganta Website dashi.

Darasin daza muyi yau shine Yadda Zaka Sayi Custome Domain A Godaddy.Com Da N1900 Kacal, Wannan farashi ba koyaushe godaddy suke badashi ba,

Suna bada wannan farashi ne ga duk wani sabon costumer wani lokaci ma farashin yana sauka har zuwa $1.17 ( kusan N500 ) amma suna bada wannan garabasa aduk karshen shekara ne.

Kamar yadda muka bata lokaci muka Rubuta wannan post muna so kaima kabata lokaci kakarantashi har karshe. Wannan rubutu shine zai kasance Jagora ga duk mai son sayen Domain A Godaddy.Com.

Ma’anar Costume Domain shine kamar .Com .Org .Net .Com.ng dakuma sauaransu, Akwai kuma free domain kamar: .tk .ga .blogspot.com da sauransu.

Custome Domain shine matakin farko dazai nuna inganci na website ko blog dinka, Amfaninta yana dayawa kadan daga ciki sune:

3. Kusan kaso 80 daga 100 suna fara yin blogging ne saboda Google Adsense, Idan kana son saurin samun Adsense Approved dole sai ka mallaki Custome Domain,

Idan kace zaka nemi Adsense Approval da free domain baza muce baza kasamuba amma zakasha wahala sosai.

4. Wani lokaci yana iya kasancewa kace zaka saida website ko blog dinka, Idan bakada Costum Domain zaiyi wahala kasamu wanda zai sayeshi da free domain.

Kokasan cewa akwai wanda aikinsu a Internet shine sayen Costum Domain da sayarwa? zaka iya sayen domain akan N500 ko kasa da haka kasayar N10000 ko sama da haka, Yadanganta da yanayin domain dinka dakuma ingancinta.

Godaddy.Com wani shahararren Website ne wanda yayi suna wajen sayar da Costum Domain har yanzu babu wani Website wanda yakai godaddy yawan wanda suka sayi Costum Domain daga nan sai Namecheap wanda yake biye dashi ayawan Domains,

Ayanzu Godaddy yanada yawan domains wanda sukayi register kusan Miliyan 19 kuma an bude wannan website tun shekarar 1999 yanada kusan shekara 20 da kafawa.

Yadda Zaka Sayi .Com Domain A Godaddy

Yanzu zamu tafi zuwa yadda zaka iya sayen Costum Domain a godaddy da N1800 kacal, Dafarko zaka bude Browser dinka ( Chrome Browser Ko Firefox ) awajen search sai karubuta godaddy promo code idan kadanna Search zakaga shafi mai kama da wannan :-

Image for post

Zakaga inda nazagaye da jan layi asama sai kashiga zaka samu kanka a wannan shafi :-

Image for post
Custome Domain

A wannan shafi zakaga inda aka rubuta Get The Perfect Domain anan zaka saka sunan domain din dakake son saya a godaddy,

Yanzu zamu misalta yadda zamu sayi custom domain a wannan shafi. Yanzu zansaka sunan domain din danake son saya kamar haka misali.com sai kadanna inda aka rubuta Search gashi kamar haka:-

Image for post

Kamar yadda kake gani a hoton dake sama nasaka sunan domain dazan saya wato misali.com yanzu idan na danna search zamu tafi zuwa shafi nagaba shine wannan:-

Image for post

Wannan shafi yanuna mana akwai domain mai suna misali.com amma wani yariga yasayeta wanda kuma yanzu yasakata a kasuwa a farashi Dala Dubu Hudu Da Dari Biyu Da Hamsin,

Don haka bazamu iya sayen wannan domain ba amma akasa ga wata mai kama da ita itace mis-ali.com farashinta Dala Biyar ( N1900 ) idan muna son sayen wannan domain sai mu danna idan aka rubuta Add To Cart

sai kaduba sama wajen Search Results zakaga inda aka rubuta Continue To Cart sai kadannashi zakaga shafi nagaba

Image for post

Kamar yadda kagani a hoton dake sama a wannan shafi zaka danna inda aka rubuta Continue To Cart sai muje gaba

Image for post

Wannan hoto danayi asama yana dauke da bayanai guda biya, Bayani nafarko shine akan domain din dazaka saya zakaga ansaka farashint $4.99 wato dala 5 ( N1900 ) sannan zakaga farashin yadda zaka sabuntata idan kwanakinta yakare farashi $18.17 wato dala 18 ( N6500 ). Bayani nabiyu shine yadda zakayi Sign In, 

Yadda zaka saka gmail account dinka domin sayen wannan domain, Idan kataba yin register da godaddy sai kashiga inda aka rubuta sign in kasaka gmail da password dinka.

Amma yanzu zamu shiga inda aka rubuta Create Account tunda muna koyarwane.

Idan kashiga yadda akace Create Account zakaga shafin daza kayi register da godaddy domin sayen wannan domain gashi a wannan hoto:-

Image for post

Zaka iya register da godaddy ta hanyoyi biyu Facebook Account ko Gmail Account, Yanzu zamuyi amfani da google account domin bude godaddy account idan kaduba kasa zakaga inda zaka saka Email, Username, Password, kamar yadda kake gani a hoton dake kasa-

Image for post

Inda aka rubuta Email sai kasaka Gmail Account dinka, Zaka iya kara saka gmail account dinka a inda aka rubuta Username kokuma kazabi wani suna wanda kakeso. Inda akace Password sai kazabi kalmomin tsaro nashiga account dinka aduk lokacin dakake so,

Wajen zaben password sai kalura dole sai kayi amfani da babban harafi aciki (capital letter) sannan dole sai kayi amfani da code irin su:- /?#* sannan kuma dole adadinsu yakai 8 ko fiye da haka.

Idan kayi kasa zakaga inda aka rubuta Agree da kuma Decline sai kadanna inda akace Agree sannan sai kadannna inda aka rubuta Create Account domin zuwa shafi nagaba

Amma zaka iya samun Security Challenge wato za a nuna maka wasu hotuna idan kajerasu dadai zaka wuce.

Image for post

Wadannan hotuna dake sama zakaga shafi guda biyu nafarko Billing Address ga bayaninsa atakaice, Ma’anar billing address shine bayanai na wanda zai sayi wannan domain wanda suke dauke acikin katin dazai sayi domain dashi wato ATM,

Awajen wadansu banki dake nigeria dole sai kasaka wadannan bayanai daidai da yadda kayi register wajen yin ATM waadansu kuma ba dole bane,

Zaka saka wadannan bayanai daidai da yadda kake zaune wato ( First Name — sunanka), ( Last Name — sunan mahaifi), ( Primary Phone — lambar wayarka), ( Address — inda kake dazama), ( Postal Code — Lambar unguwarka ko yankinka), ( State — jahar dakake) ( City — garin dakake),

Shafi nabiyu shine Your Items, Wannan shafi yana dauke da bayani na domain daza kasaya, zakaga Website Builder Free Trial wannan bashida amfani cikin bayaninmu nayau,

Zakaga sunan domain din daza kasaya katabbatar kasaitata zuwa shekara daya kamar haka 1 Year. 

Zakaga Full Domain Privacy & Protection shima kawuceshi akarshe katabbar kaga farashi yayi daidai da Total (USD) $4.99 sai kadanna inda aka rubuta Save zakaga wannan shafin:-

Image for post

Yanzu munzo gurin saka ATM Details wato bayanai na katin daza kasayi wannan domain dashi, Abin lura: bakowane ATM Card ne godaddy suke karba ba,

ATM dazaka iya aiki dashi a godaddy sune Visa, Mastercard, Discover, da sauransu. Idan kana da daya daga cikin wadannan ATM to ga yadda zakayi amfani dashi:-

Zakaga Card Number sai kasaka lambobin ATM dinka ( zaka gansu jikin katin guda 16 ) sai Expiration wata da kuma shekarar da ATM din zai kare ( zaka gani jinkin ATM dinka ) sai Security Code wasu lambobine guda 3 ( zaka gansu abayan ATM dinka daga sama ) kana gama saka wannan bayanai sai kadanna Save zakaga shafi nakarshe yabude kamar haka:-

Image for post

Yanzu sai kadanna inda aka rubuta Compelete Purchase shikenan godaddy zasu chajeka N1800 daga nan zaka samu sakon cewa kasayi wannan domain acikin gmail dinka,

Yanzu sai yadda zaka dora wannan domain akan blogger ko wordpress wanda insha allahu anan gaba kadan zamu kawo muku yadda ake dora godaddy domain a blogger.

Zaku iya join da shafin hausatechs na facebook Click Here kokuma zaku zaku iya magana damu ta watsapp da wannan lamba 07066870719, Mungode

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *