Yadda Zaka Hada National Identity Number Da Layin MTN, Airtel, Glo, 9Mobile

Yadda Zaka Hada National Identity Number Da Layin MTN, Airtel, Glo, 9Mobile

Kamar yadda sanarwa ta karade shafukan sada zumunta cewa hukumar NCC tayi gargadin cewa zata rufe duk layin wayar da ba a hadashi da katin dan kasa ba (National Identity Number) cikin sati biyu.

Sanarwar tasa yan Nigeria dadama sun shiga cikin rudani da kuma tsoron abin dazai je yadawo wajen rasa layukan wayarsu, Ganin yadda NCC tabada lokaci kadan wajen hada layin waya da National Identity Number.

Manyan kamfanonin sadarwa kamar MTN, Airtel, Glo, 9Mobile sun fitar da yadda mutum zai hada layinsa da katin dan kasa batare da yaje office ba, Sun kawo hanyar daza kayi amfani da wayarka cikin sauki domin gujewa cunkoso.

Duba Wannan: Hukumar NCC Tahana MTN Da Airtel Glo Sayar Da Sabbin Layukan Waya

Yadda Zaka Duba Lambar Katin Dan Kasa Da Wayarka

Dafarko kafin kayi wannan verification dole sai kanada lambar katinka na dan kasa a hannu, zaka iya duba wannan Number da kowane layin waya kake amfani.

Idan kadanna *346# za a nuna maka yadda zaka danna 1 domin ganin lambar amma ana chajin N20 domin yin hakan.

Yadda Zaka Hada Layin MTN da National Identity Number

MTN sun fitar da hanyoyi guda biyu wajen yin abin, hanya tafarko sun bada wani link wanda zaka cike duk abin da ake bukata wajen yin wannan verification cikin sauki.

Dafarko zaka shiga wannan Link sai kasaka wadannan abubuwa:

First Name

Last Name

Middle Name (idan kana dashi)

Phone Number

National Identity Number

Email Address (idan kana dashi)

Sai kadanna Submit, shikean sai kajira zaka samu sako daga MTN idan verification dinka yayi ko a a.

Yadda Zaka Hada National Identity Number Da Layin MTN, Airtel, Glo, 9Mobile

Hanya ta biyu da MTN yafitar itace amfani da Code wato lambobi, wannan hanyar baka bukatar babbar waya ko karamar waya wanda bata da internet zata iya maka.

Kawai zaka danna *785* lambar katin dan kasa sai # kamar dai haka *785*1234567890# sai katura zasu hada layinka da National Idetity Number dinka.

Yadda Zaka Hada layin Airtel da National Identity Number

Idan kanada layin Airtel zaka iya wannan hadi ciki sauki, kawai zaka danna *121# zasu nuna maka inda zaka zabi 1 domin saka lambar katin dan kasa sai kadanna.

Zasu nuna maka shafi nagaba sai kasaka lambobin katin dan kasarka sai kadanna Send shikenan kajira sako da Airtel.

Yadda Zaka Hada layin Glo da National Identity Number

Domin hada layin Glo da katin dan kasa domin gujewa rufe layin zaka tura sako zuwa wata lamba su kuma Glo zasu hada katin da lambar layinka.

Dafarko zaka shiga wajen rubuta Message a wayarka sai karubuta haka: “UpdateNIN lambar katin dan kasa sunanka sunan mahaifinka (kamar dai yadda yake ajikin katin dan kasarka) sai katura zuwa 109

Gashi atakaice: Send “UpdateNIN 1234567890 Ibrahim haruna to 109” shikenan Glo zasu hada layinka da National Identity Number dinka.

Har yanzu layin 9Mobile basu fitar da yadda zakayi wannan verification da wayar hannu ba, Don haka dole sai kaje office dinsu domin hada maka layinka da National Identity Number.

Kada kamanta katafi da lambar katinka na dan kasa zuwa office dinsu, zaka iya duba wannan Number da kowane layi idan kadanna *346# amma ana chajin N20 dafatan kagane.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *